Isa ga babban shafi
Guinea-Bisseau

Yan Majalisu Guinee Bissau sun amince da kasafin kudin kasar

Yan Majalisun kasar Guinee Bissau a jiya asabar sun cimma matsaya tareda amincewa da kasafin kudin shekarar bana watanni biyu bayan samar da gwamnatin hadin gwiwa.

Aristides Gomes, Firaministan kasar Guinee Bissau
Aristides Gomes, Firaministan kasar Guinee Bissau Lusa
Talla

Daga cikin yan majalisu 102, yan Majalisu 90 suka amince da kasafin kudin kasar na bilyan 212 na kudin Cfa ko euros milyan 324.

Tun a watan Agustan shekarar 2015 ne aka soma kai ruwa rana a wannan kasa tun bayan da Shugaban Kasar Jose Maria Vaz ya salami Firaministan sa Domingos Simons Perreira.

Samar da kasasfi kudin kasar dama amincewar sa daga yan Majalisa zai taimakawa gwamnatin wajen sake dawo da martabar kasar a idanu duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.