Isa ga babban shafi
Mali-Makiyaya

Mali ta fara bincike kan sanadin kisan Makiyaya 32

Gwamnatin Mali ta kaddamar da bincike domin gano musababbin faruwar rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar Fulani makiyaya 32 a wani kauye mai suna Koumaga da ke tsakiyar kasar.

A cewar Kakakin gwamnatin ta Mali duk da cewa gwamnati na iya kokarinta wajen samar da zaman lafiya mai dorewa, ya zama wajibi shugabannin al’umma su shigo a cikin wannan batu domin samar da zaman lafiya a Mali.
A cewar Kakakin gwamnatin ta Mali duk da cewa gwamnati na iya kokarinta wajen samar da zaman lafiya mai dorewa, ya zama wajibi shugabannin al’umma su shigo a cikin wannan batu domin samar da zaman lafiya a Mali. © Samuel Turpin/HCCS
Talla

Bangarori da dama dai na zargin maharban gargajiya daga kabilar Dogon da aikata kisan, ko da dai kakakin gwamnatin kasar ta Mali Amadou Koita, ya ce bincike ne kadai ne zai tattabar da wadanda suka aikata kisan.

A cewar Amadou Koita ya ce ‘yan ta’adda na amfani da damar rikicin tsakanin kabilun 2 ta hanyar zuga su afka wa juna.

Sai dai Mr Koita ya ce ba zai iya cewa kome game da zargin da ake yi wa maharban gargajiya da ake kira Dozo ba inda ya sha alwashin gudanar da cikakken bincike don gano wadanda ke da hannun wajen kai harin.

Amadou Koita ya ce gwamnati za ta tabbatar ganin an hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan rikici, yana mai cewa fatansu shi ne samar da zaman lafiya, inda ya yi amfani da damar wajen kara yin kira ga jama’a don neman hadin kai

A cewarsa duk da cewa gwamnati na iya kokarinta wajen samar da zaman lafiya mai dorewa, ya zama wajibi shugabannin al’umma su shigo a cikin wannan batu domin samar da zaman lafiya a Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.