Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta kudu

Salva Kirr da Rieck Machar sun sake ganawa a Karo na 2

A yau litinin, shugaban Sudan ta Kudu Salva Kirr da babban abokin hamayyarsa na siyasa Rieck Machar sun sake ganawa amma wannan karo a birnin Khartum na kasar Sudan, a yunkurin kawo karshen yakin basasar kasar.

Ganawar ta yau ta zo ne kasa da mako daya da Salva Kirr da kuma Rieck Machar suka hadu a birnin Adis Ababa na kasar Habasha karon farko a cikin sama da shekaru biyu.
Ganawar ta yau ta zo ne kasa da mako daya da Salva Kirr da kuma Rieck Machar suka hadu a birnin Adis Ababa na kasar Habasha karon farko a cikin sama da shekaru biyu. Presidential Press Service/Handout via REUTERS
Talla

Ganawar ta yau ta zo ne kasa da mako daya da Salva Kirr da kuma Rieck Machar suka hadu a birnin Adis Ababa na kasar Habasha karon farko a cikin sama da shekaru biyu.

Shugaban Sudan Omar Hasan al-Bashir ne ke jagorantar taron na yau da nufin kawo karshen rikcin da ake fama da shi shekaru dudu da rabi a wannan kasa da ba ta jima da samun ‘yancin kanta ba.

Ko baya ga shugaban Omar al-Bashar, a wannan karo taron na samun halartar shugaban Uganda Yuweri Musaveni, wata alama da ke kara tabbatar da cewa kasashen yankin sun damu da halin da makociyarsu Sudan ta Kudu ke ciki.

To sai dai bayan ganawar farko da Salva Kirr da Machar suka suka yi a birnin Adis Ababa cikin makon jiya, gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce ta fara kosawa da halayen tsohon mataimakin shugaban kasar, saboda haka ba za ta amince da ba shi matsayi a sabuwar gwamnatin hada-ka da za a kafa a nan gaba ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.