Isa ga babban shafi
Mali

Dakarun Minusma da G5 Sahel sun kashe fararen hula a Mali

Masu bincike na rundunar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali Minusma, sun tabbatar da zargin da ake yi wa dakarun kasar ta Mali da na G5 Sahel na kashe fararen hula a yankin Boulikessi da ke tsakiyar kasar ba tare da sun aikata wani laifi ba.

Shalkkwatar rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta Minusma a garin Gao na Mali
Shalkkwatar rundunar Majalisar Dinkin Duniya ta Minusma a garin Gao na Mali RFI/Olivier Fourt
Talla

Lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan mayun da ya gabata, inda sojoji suka kai farmaki a kan wata kasuwar sayar da dabbobi tare da kashe fararen hula 12 a garin na Boulikessi da ke gaf da iyakar Mali da Burkina Faso.

Sojoji sun kai hari a kasuwar ne bayan kashe daya daga cikin sojojin a wannan yanki mai fama da ‘yan bindiga.

To sai dai lokacin da lamarin ya faru, ma’aikatar tsaron Mali ta bayyana cewa an kashe fararen hular ne a wani artabu da dakarun na Mali da kuma na G5 Sahel, kafin daga bisani bincike ya tabbatar da cewa an kashe mutanen ne a cikin kasuwa ba tare da sun aikata wani laifi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.