Isa ga babban shafi
Kamaru

Tsawaita wa'adin aikin 'yan majalisar Kamaru da shekara daya

Gwamnatin Kamaru ta gabatar wa ‘yan majalisar dokokin kasar da wani daftari da ke neman tsawaita wa’adin aikin ‘yan majalisar har tsawon shekara daya bayan karewar wa’adinsu.

Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban Kamaru Paul Biya REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Daftarin da gwamnati ta gabatar wa majalisar a ranar 26 ga wannan wata na yuni, ya ce akwai bukatar tsawaita wa’adin ‘yan majalisar ne domin rage yawan zabubukan da ya kamata a gudanar  shekarar bana a kasar da suka hada da zaben ‘yan majalisa, shugaban kasa da kuma kananan hukumomi.

A ranar 29 ga watan oktoban 2018 ne wa’adin aikin ‘yan majalisar zai kawo karshe, to amma daftarin da gwamnatin ta gabatar na neman tsawaita shi zuwa 29 ga watan oktoban 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.