rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Lagos

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana fargabar mutuwar tarin jama'a bayan konewar fiye da motoci 30 a Lagos

media
Hukumomi dai a jihar ta Lagos sun yi ta amfani da gidajen rediyo wajen sanar da tarin matafiya su kaucewa hanyar musamman la’akari da yadda abin ya faru a dai dai lokacin da tarin ma’aikata ke dawowa daga aiki. rfihausa

Wata gagarumar wuta da ta faro sanadiyyar hadarin tankar mai a jihar Lagos da ke kudancin Najeriya ta kone tarin motoci da turakun lantarki da ke kan kan hanyar Lagos zuwa Ibadan. Kawo yanzu babu adadin mutanen da suka mutu a gobarar sai dai akwai fargabar samun adadi mai yawa.


Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar ta Lagos LASMA ta ce al’amarin ya faru ne sanadiyyar wata tankar dakon mai da tun farko da kama da wuta tare da harbuwa ga tarin motoci fiye da 30 dake kan gadar.

Rahotanni na nuni da cewa Tankar man ta kubcewa matukin ta ne wanda ke kokarin wuce wata mota.

Hukumar kashe gobara tare da hadin gwiwar hukumar ta LASMA sun ce suna gudanar da aikin ceton rai la’akari da tarin motocin da abin ya shafa.

Cikin bayanan da ta wallafa a shafinta na Twitter LASMA ta ce yanzu haka jami’anta na ci gaba da aiki don tabbatar da ganin an tseratar da tarin rayukan da gobarar ta rutsa da su.

Shaidun gani da Ido sun tabbatar da yadda mutanen da ke kan gadar da dama suka rika fita suna barin motocinsu don tsira da rayukansu.

Hukumar kare afkuwar hadurra a Najeriyar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta bukaci matafiya su kauracewa hanyar.

Hukumomi dai a jihar ta Lagos sun yi ta amfani da gidajen rediyo wajen sanar da tarin matafiya su kaucewa hanyar musamman la’akari da yadda abin ya faru a dai dai lokacin da tarin ma’aikata ke dawowa daga aiki.

Daraktan hukumar agajin gaggawa na jihar Lagos Rasaki Musibau ya ce motar na shake da man fetur ne lokacin da hadarin ya afku.