Isa ga babban shafi
Mali-G5 Sahel

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 6 Shalkwatar G5 Sahel

Wani harin kunar bakin wake da aka kai shalkwatar rundunar G5 Sahel mai yaki da ta'addanci a kasashen Sahara 5 yau Juma'a ya hallaka akalla mutane 6 yayinda wasu da dama kuma suka jikkata.Wannan ne karon farko da rundunar ke fuskantar hari tun bayan kafa ta a shekarar 2017 da nufin dai dai zaman lafiyar yankin da ke fuskantar barazanar tsaro.  

Wannan ne karon farko da rundunar ke fuskantar hari tun bayan kafa ta a shekarar 2017 da nufin dai dai zaman lafiyar yankin da ke fuskantar barazanar tsaro.
Wannan ne karon farko da rundunar ke fuskantar hari tun bayan kafa ta a shekarar 2017 da nufin dai dai zaman lafiyar yankin da ke fuskantar barazanar tsaro. SEBASTIEN RIEUSSEC / AFP
Talla

Rahotanni sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya kutsa kan shi cikin harabar shalkwatar rundunar da ke kasar Mali tare da tayar da bom din da ke jikinsa.

Kawo yanzu adadin mutane 6 aka tabbatar da mutuwarsu yayinda ake ci gaba da aikin bayar da agajin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Wani ganau da ke sana’ar sayar da lemon zaki a gab da shalkwatar ta G5 Sahel a tsakiyar kasar Mali Haoussa Haidara ya ce masayar wuta ta biyo bayan fashewar Bom din wadda aka dauki tsawon sa’a guda ana yi.

Harin dai na zuwa ne kwana uku gabanin wani taro tsakanin shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban rundunar G5 Sahel da zai gudana a Nouakchott babban birnin Mauritania.

Rundunar G5 Sahel dai rundunar hadin gwiwa ce ta kasashen Mali Nijar Chadi, Mauritania da kuma Burkina Faso wadda ke samun tallafin Faransa dama Majalisar Dinkin Duniya don yaki da ta'addanci a yankin na Sahel.

Kawo yanzu dai ba a tantance su waye wadanda harin ya rutsa da su ba, haka zalika babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.