rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwankwaso yace zai kada Muhammadu Buhari a zabe

media
Tsohon Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso tareda gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje NAIJ Nigeria

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce muddin Jam’iyyar PDP ta bashi tikitin takarar zaben shugaban kasar shekara mai zuwa babu abinda zai hana shi kada shugaba Muhammadu Buhari.


Yayin wata hirar da akayi da shi a karshen makon nan, Kwankwaso yace yanzu haka bashi da jam’iyya, kuma zai gwada sa’ar sa a wani wuri na daban saboda yadda Jam’iyyar APC tayi watsi da shi, duk da gudumawar da ya bayar wajen samun nasarar ta da kuma shugaba Buhari a zaben da ya gabata.

Sanatan yace ya san Jam’iyyar PDP babbar Jam’iyya ce, kuma muddin ta gudanar da zaben fidda gwani mai inganci kamar yadda dimokiradiya ya tanada, tana iya kada Buhari a cikin sauki.

Kwankwaso yace PDP tana bukatar dan takara daga Jihohin Katsina da Kaduna da Kano domin samun nasarar zabe mai zuwa saboda yawan masu kada kuri’un da Jihohin ke da su.

Tsohon Gwamnan ya kauracewa taron Jam’iyyar APC da ya gudana a Abuja, yayin da ake ganin sa yana ganawa da wasu jiga jigan Jam’iyyar PDP cikin su harda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Ekiti Ayo Fayose.