rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya za ta rabawa talakawa kudaden da Abacha ya boye a Ketare

media
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Sani Abacha. AFP

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa za ta fara aikin rarrraba kudaden da tsohon shugaban kasar na mulkin soja janar Sani Abacha ya wawashe daga lalitar kasar tare da boyewa a kasashen Turai ga tarin talakawanta.


Gwamnatin ta ce za ta fara aikin ne a wata mai zuwa na Yuli da zarar hukumomin Switzerland suka dawo da kudaden da yawansu ya haura dala miliyan 300.

Kudaden wanda tsohon shugaban ya wawashe a shekarar 1990 za a yi aikin rabawa akalla magidanta dubu dari 3 a jihohin kasar 19 inda kowannesu zai rika samun dala 14 a wata guda.

Babu dai cikakken bayani kan jihohin da za a rabawa kudin haka zalika babu takamaiman nau'ikan mutane da za su ci gajiyar kudaden.