rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu daga ciki da wajen Najeriya ke tinzira tashe tashen hankulan kasar

media
Janar Tukur Yusuf Buratai Shugaban rundunar sojin Najeriya thenewsnigeria

Shugaban rundunar sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya yi zargin cewar wasu daga ciki da wajen kasar ke tinzira tashe tashen hankulan da ake samu a Jihar Filato da wasu jihohin kasar.


Janar Buratai wanda ya bayyana kashe kashen a matsayin mummunar rashin hankali, ya ce rundunar sojin kasar da takwarorin ta na tsaro na iya bakin kokarin su wajen ganin sun magance sake aukuwar lamarin.

Shugaban sojin ya ce suna sane da manyan kalubalen tsaron da suka addabi Najeriya a shekaru 10 da suka wuce, kuma rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara wajen ayyukan ta.

Janar Buratai yayi zargin cewa akwai kungiyoyin da dama a ciki da wajen Najeriya dake tinzira tashin hankalin da ake samu domin ganin kasar ta dare, inda yake cewa yanzu ba lokaci ne nuna yatsa tsakanin kabila ko addini ba, sai dai hada kai domin magance matsalar.