rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rundunar G5 ta sha alwashin kara karfafa yakar ta'addanci

media
Gaban ginin hedikwatar rundunar hadin gwiwa ta G5 Sahel da aka kai wa hari a Mali. AFP/STRINGER

Rundunar hadin gwiwar kasashe 5 ta G5 Sahel ta sha alwashin kara kaimi wajen yakar ta’addanci a yankin na Sahel, bayan hallaka dakarunta akalla 6 da aka yi a wani hari da aka kai kan hedikwatar ta a ranar Juma’a da ta gabata.


Wani dan kunar bakin wake ne ya gabza motar da ya ke ciki mai makare da bama bamai a gaban ginin hedikwatar ta G5 Sahel.

Sai dai yayin tsokaci akan harin ministan harkokin waje na Mauritania Isma’il Ould Shiekh Ahmed, ya ce babu tsirin da harin zai yi, illa karawa kungiyar karfi da kuma jajircewa.

Harin na ranar Juma’a ya zama irinsa na farko da aka kai wa hedikwatar rundunar hadin gwiwar, tun bayan kafa ta da aka yi da taimakon kasar Faransa a shekarar 2017, domin kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin Sahel.

Rundunar ta kunshi dakarun kasashe daga Mali, Nijar, Chadi, Mauritania da kuma Burkina Faso.