rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Mauritania

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabannin kasashen Afrika na taro a Mauritania

media
Wasu shugabannin kasashen nahiyar Afrika da ke karkashin kungiyar AU. Tiksa Negeri/Reuters

A yau Lahadi ake soma taron kwanaki 2 na shugabannin kasashen Afrika a Nouakchott, babban birnin kasar Mauritania.


Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan manyan batutuwan da suka hada da, yaki da cin hanci da rashawa, kawo karshen matsalolin tsaro na rikicin kabilanci da ta’addanci, sai kuma tattaunawa kan inganta huldar kasuwanci da kuma samar da alakar cinikin bai daya.

A gefe guda kuma wakilan kungiyar kasashen Afrikan AU, zasu tattaunawa kan warware rikicin sudan ta kudu, da kuma maido da kyakkyawar dangantaka tsakanin Habasha da Eritrea, wadanda tuni gwamnatocin kasashe biyu suka soma yunkurin hakan.

Gabannin taron na yau Lahadi, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar kasashen Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci daukar matakan ladabtarwa, kan wadanda ke dauke da nauyin mutunta sulhun da aka cimma tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudun da kuma ‘yan tawayen kasar, wato, shugaba Salva Kiir da madugun 'yan tawaye Riek Machar.

A ranar Asabar da ta gabata, a ranar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakaninsu ta soma aiki, dakarun Sudan ta Kudu da ‘yan tawayen kasar, suka kai wa junansu hare-hare.

Kakakin mayakan ‘yan tawayen Lam Paul Gabriel, ya ce sojin gwamnati sun fara kai hari ne kan sansaninsu da ke kauyen Mboro da ke arewa maso yammacin kasar, abinda ya sa suka maida martani, ta hanyar kai wa dakarun kasar hare-hare a jihohin kasar guda hudu.

A ranar Larabar da ta gabata, shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir da madugun ‘yan tawaye Riek Machar, suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, da suka cimma a gabanawar da suka yi a kasar Habasha.