rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan gudun hijirar Kamaru sun watsi da tallafin gwamnati

media
Wasu 'yan kasar Kamaru da ke gudun hijira a sansanin Bashu-Okpambe, da ke jihar Cross Rivers, a kudancin Najeriya. PIUS UTOMI EKPEI / AFP

‘Yan kasar Kamaru da ke gudun hijira a Najeriya sakamakon rikicin ‘yan awaren kasar, sun ce ba zasu amince da karbar duk wani tallafin taimako daga gwamnatin Kamaru ba, wanda ta ke shirin kai musu.


Tuni dai aka tara miliyoyin kudin CFA a gidauniyar da gwamnatin Kamaru ta kafa domin bai wa ‘yan gudun hijirar akalla dubu 22 tallafi, wadanda suka tsere zuwa Najeriya, a dalilin rikicin ‘yan awaren kasar.

Sai dai cikin wata wasika da shugabannin ‘yan gudun hijirar masu amfani da harshen Ingilishi, suka aika wa hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, sun bayyana dalilan da suka sanya su daukar matakin kin karbar tallafin daga gwamnatin Kamaru.

A cewar ‘yan gudun hijirar, abinda suke bukata shi ne magance tushen matsalar da ya haddasa rikicin ‘yan awaren ba wai samun tallafin abince ba.

Daga cikin dalilan da ‘yan gudun hijirar suka bayyana akwai, ci gaba da tsare shugaban yunkurin samar wa yankuna masu amfani da Ingilishi ‘yancin kai daga Kamaru, Sisiku Ayuk Tabe da mataimakansa a kurkuku, inda suka bukaci sakin fursunonin yankin ‘yan awaren da gwamnati ta kama.

Zalika ‘yan gudun hijirar na Kamaru da ke Najeriya, sun bukaci gwamnatin kasar ta soma tattaunawa da masu fafutukar ballewa daga kasar, a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.