rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An gurfanar da wasu mutane uku, kan fashewar wata madatsar ruwa a Kenya

media
wani jami'in soja na duba barnar da ruwa suka haddasa bayaan fashewar wata madatsar ruwa a garin Solail, na kasar Kenya, a ranar 10 mayu na 2018. REUTERS/Thomas Mukoya

Gwamnatin kasar Kenya ta tuhumi mutane 3 da aikata laifin kisa, saboda zargin da ake musu na yin sakacin da yayi sanadiyar fashewar wata madatsar ruwa da ta share wasu gonakin Flawa, da gidajen zaman jama'a  a garin Solai dake Yankin Nakuru a watan mayun da ya gabata, lamarin da ya haddasa mutuwar akalla mutane 47.


Mutanen sun hada da babban shugaban da ke kula da madatsan ruwan, Perry Kansagara, da shugaba Vinoj Kumar, da kuma jami’in dake kula da harkokin ruwan yankin, Johnson Njuguna, wadanda aka gurfanar a babbar kotun kasar da ke Rift Valley a Naivasha.

Ofishin da ke gurfanar da masu aikata laifuka na kasar Kenya, ya wallafa a shafinsa na tweeter cewa, wadanda ake tuhuma sun musanta zargin da ake musu na cewa suna da hannu a lamarin da ya haddasa asarar rayuka da dama, sakamakon rashin mayar da hankali wajen tafiyar da aikin su, da rashin bada rahoto dangane da illolin da madatsan ruwan ke yi wa muhalli.

Babban mai gabatar da karar kasar ta Kenya Noordin Haji, ya bada umarnin gurfanar da mutane 9 da suka hada da yan kasuwa da wasu jami’an gwamnati saboda an zarge su da yin sakaci wajen aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata. Ya kuma kara da cewa, mutane 3 na farko ne aka fara tuhuma, sannan suka bukaci kotu da ta bada sammacin kama sauran mutane shida.

Haji ya ce wadanda suka gina madatsar ruwan ba kwararru bane, kuma sunyi amfani da kayayakin marasa inganci wajen gina ta, da kuma rashin mayar da hankali ga illolin da madatsan ruwan ke yi wa muhalli.