rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Somalia Al Shebaab Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mayakan Al Shabaab sun sake kai hari a birnin Mogadishu

media
Jami'an tsaron Somalia a birnin Mogadishu, yayin da suke kokarin yi wa harabar da dan kunar bakin wake ya tarwatsa wata mota kawanya. REUTERS/Feisal Omar

Rundunar ‘yan sandan Somalia ta ce tagwayen hare-haren bam da aka kai kan ma’aikatar tsaron cikin gidan kasar da ke birnin Mogadishu, sun yi sanadin hallakar fararen hula 5 da jami’in dan sanda daya.


Harin dai shi ne na baya bayan nan da kungiyar al Shebaab ta yi dauki alhakin kai wa a kasar ta Somalia.

Kwamandan ‘yan sandan birnin Mogadishu, Ibrahim Muhd, baya ga wadanda suka hallaka, akalla mutane 21 sun jikkata a harin, sai dai sun yi nasarar hallaka baki dayan mayaka hudu na kungiyar ta Al Shebaab da suka kai harin ciki harda dan kunar bakin wake daya.

Duk da rasa yankunan da ta kame a baya, bayan shafe sama da shekaru 10 tana kokarin kawar da gwamnatin Somalia, har yanzu kungiyar al Shebaab na samun karfin kai hare-haren kunar bakin wake da kuma samamen ‘yan bindiga kan ma’aikatun gwamnatin kasar da kuma wuraren cinkoson fararen hula.