rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Buhari ya jaddada alwashin kawo karshen Boko Haram

media
Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya ziyarci garin Mongunou dake da nisan kilometa 140 da Maiduguri ya bayyana cewa ana daf da kawo karshen kungiyar Boko Haram da ma haren haren kungiyar a Najeriya.


Kawar da kungiyar Boko Haram na daya daga cikin alkawuran da Shugaban na Najeriya ya yi wa yan kasar yau da shekaru uku da suka gabata, gani ta yada kungiyar ta daidaita wasu yankunan arewacin Najeriya, tilastawa mutane tserewa daga gidajen su, kisan sama da mutane 20.000, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mayar da hankali wajen sake gina wadanan yankuna tareda ci gaba da tabbatar da tasro ne manyan ayukan da za su gaba. Sai dai wani babban kalubale dake gaban Shugaban shine batun kawo karshen tashin hankali da ake fuskanta tsakanin manoma da makiyaya