rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wata mata da ke taimakawa masu tada kayar baya ta shiga hannu

media
Wasu daga cikin dakarun majalisar dinkin duniya da ke sintiri a garin Kouroume, da ke arewacin kasar Mali. REUTERS/Adama Diarra

Jami’an tsaron farin kaya na Mali sun kama wata mata ‘yar kasar bisa aikata laifin taimakawa mayaka masu tada kayar baya ta hanyar basu takin zamani da suke amfani da shi wajen hada bama-bamai.


Karo na farko kenan da jami’an tsaron mali suka kama wata mace da aikata irin wannan laifi a kasar.

Matar wadda ta shiga hannu a ranar Alhamis da ta gabata, ta fito ne daga garin Mopti da ke tsakiyar kasar ta Mali, yankin da a baya bayan nan ya yi fama da hare-haren ta’addanci ta hanyar amfani da bama’bamai kirar gargajiya.

Kawo yanzu masu bincike basu bayyana iyaka yawan takin da matar ke yiwa mayakan safara ba, wanda suke amfani da shi wajen hada nakiyoyin da suka binnewa da kuma bama-bamai.