rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Hakkin Dan Adam Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yawaitar take hakkin dan adam a Congo ya wuce kima - MDD

media
Dakarun Jamhuriyar Congo a gaf da garin Kiwanja da ke yankin gabashin kasar. Reuters

Hukumar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya, ta ce ana tafka munanan laifukan cin zarafin dan adam yankin kasai na Jamhuriyar Congo, inda ta bayyana shirin aika tawagar kwararru don bincika halin da ake ciki a yankin.


Cikin rahoton baya bayan nan da aka wallafa, jami’an hukumar ta kare hakkin dan adam sun zargi sojojin jamhuriyar Congo da ‘yan tawaye da sauran kungiyoyin mayakan sa kai, da aikata laifukan yi wa fararen hula kisan gilla a yankin na Kasai, aikata fyade, bautar da jama’a da dai sauran laifukan take hakkin dan adam.

A watan Satumba na shekarar 2016, rikici ya barke a yankin na Kasai, bayan da sojojin kasar suka kashe Kamwina Nsapu, wani jagoran al’ummar yankin da ya yi kaurin suna wajen adawa da gwamnatin Joseph Kabila.

Wannan ce ta bai wa wasu mayakan sa kai damar fara tada kayar baya, inda suke yakar gwamnatin da sunan jagoran al’ummar.