rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyoyin Mujami'u sun sha alwashin kawar da Joseph Kabila

media
Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo REUTERS/Kenny Katombe

Kungiyar shugabannin darikar Katolikan Jamhuriyar Congo Dimokuradiyya sun gayaci yan kasar da su kasance cikin shirin ko ta kwana domin tilastawa Shugaban kasa Joseph Kabila sauka daga kujerar Shugabancin kasar.


Kungiyar ta sanar da cewa ta na cikin shiri wajen shirya gangami na kwanuki uku da hurumi tilasatawa Kabila sauka, kama daga ranakun 12,13 da 14 ga watan Agusta shekarar bana.

A hukumance gwamnatin kasar ta shirya domin gudanar da zabukan kasar, wanda hukumar zabe ta bayyana ranar 8 ga watan Agusta rana ta karshe ga yan takara a zaben Shugabancin kasar don su yi rijista.