rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Cote d'Ivoire Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwararru kan tsirrai na taro kan cutar Ebolar Rogo

media
Cutar Ebolar Rogo na barazanar jefa miliyoyin jama'a a nahiyar Afrika cikin bala'in yunwa. AFP/ PIUS UTOMI EKPEI

Kwararru a fannin noma da ilimin tsirrai daga kasashen yammacin nahiyar Afrika 6, na taro a birnin Abdijan na kasar Ivory Coast, domin lalaubo hanyar kawo karshen wata cuta da ke barazana ga rogo a yankin.


Masanan sun fito ne daga kasashen Benin, Burkina- Faso, Ghana, Najeriya, Togo da kuma Ivory Coast.

Cutar da a turance ake gajarce sunanta da CBSD, masana sun bayyana cewar tana iya haddasa fadawar miliyoyin jama’a cikin bala’in yunwa musamman a yammacin nahiyar Afrika, wannan ce ta sa masana sanyawa cutar sunan Ebolar rogo.

An fara gano wannan cuta ta Ebolar rogo ne a kasar Tanzania kimanin shekaru 80 da suka gabata, wadda zuwa yanzu ta haddasa nakasu ga akalla kashi 90 na noman rogo a yankin tsakiyar Afrika.

A shekarun 1990 akalla mutane 3,000 ne suka hallaka sakamakon bala’in yunwa a kasar Uganda kasai, bayanda wanna cuta ta Ebolar rogo ta bayyana a kasar, wadda ta fi shafar kananan manoma.

Masana sun tabbatar da cewa wani kwaro da ake kira da Silverleaf whitefly ke kan gaba wajen haddasa wannan annoba.