rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha Eritrea Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Habasha da Eritrea sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu

media
Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed a bangaren hagu, tare da shugaban Eritrean Isaias Afwerki yayin rattaba hannu kan kawo karshen yakin da kasashen biyu suka shafe shekaru suna gwabzawa. 9 ga watan Yuli, 2018. Twitter/Yemane G. Meskel

Shugabannin Habasha da Eritrea sun sanya hannu kan yarjejeniyar sulhunta rikicin kan iyakar da ya lalata dangantakarsu a baya.


Ministan yada labaran Eritrea Yemane Gebremeskel ya bada wannan tabbacin a yau Litinin 9 ga watan Yuli na shekarar 2018.

An dai cimma wanan yarjejeniya ce kwana guda, bayan da Fira Ministan Habasha Abiy Ahmed ya fara ziyara a Eritrea domin ganawa da takwaransa Isaias Afwerki kan kawo karshen tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Yarjejeniyar sulhun ta kasashen suka cimma, ta kunshi ginshikai biyar.

Ginshiki na farko shi ne tabbacin kawo karshen yakar juna a hukumance, bisa rikicin iyakar da suka shafe shekaru suna gwabzawa.

Sauran batutuwan da yarjejeniyar ta Eritrea da Habasha ta kusa sun hada da shelar shiga sabon zangon zaman lafiya da juna inda daga yanzu bangarorin biyu, za su rika aiki tare wajen karfafa dangantakar siyasa, tattalin arziki, al’adu da kuma tsaro a tsakaninsu.

Sauran batutuwan da kasashen suka cimma su ne, kulla alakar kasuwanci, da sufuri sai kuma bunkasa fannin sadarwa.

A Ranar Lahadin da ta gabata, 8 ga watan Yuli na shekarar 2018, Fira ministan Habasha Abiy Ahmed, ya fara ziyara a Eritrea domin ganawa da takwaransa Isaias Afwerki a babban birnin kasar Asmara a kokarin maido da kyakkyawar dagantaka tsakaninsu.

A ganawarsu ta farko shugabannin sun mayar da hankali ne batun sulhunta rikicin kan iyaka da ke garin Badme na tsakanin kasashen biyu, wanda Habasha ta ki janye sojinta daga wajen.

A shekarar 1998 zuwa 2000 ne kazamin rikici ya barke tsakanin kasashen biyu, kan rkicin iyakar, yakin da ya yi sanadin hallakar kimanin mutane dubu 80, 000 daga dukkanin bangarorin biyu.

Tun bayan zama sabon Fira Ministan Habasha a watan Afrilu na shekarar 2018, Abiy Ahmed ya sha alwashin kawo karshen wannan tsamin dagantaka.