An kashe 'yan sanda a yankin 'yan aware
Akalla jami’an 'yan sanda biyu aka hallaka a Jamhuriyar Kamaru a ranar Litinin bayan wani hari da aka kaddamar mu su a birnin Buea da ke yammacin kasar .
Wallafawa ranar:
Sai dai wata majiyar asibiti ta shaida cewa, jami’an ‘yan sanda biyar ne aka kashe da kuma farar hula guda.
Wannan dai na kara haifar da fargaba game da kazancewar rikici tsakanin jami’an tsaro da ‘yan awaren da ke dauke da makamai a fafutukarsu ta ganin yankinsu mai amfani da Turancin Ingilishi ya samu ‘yanci daga kasar.
Bayanai na cewa, a karon farko kenan da ake kai hari a birnin Buea da ya kasance cibiyar yakin neman ballewar ‘yan awaren.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu