rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sahel Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen Afrika ta Yamma na bukatar agajin abinci

media
Kasashen yankin Sahel Wikimedia commons/LeGrandJardin

Wasu Kasashen Afirka ta Yamma guda 8 sun bukaci taimakon agajin gaggawa na abinci ga wasu kasashe 4 na yankin Sahel dake fuskantar barazanar yunwa sakamakon tashin hankalin da ake fama da shi a cikin kasashen.


Sanarwar dake zuwa bayan taron da ministocin ayyukan noma da suka fito daga kasashen Benin, Burkina Faso, Cote d’Ivoire, Mali, Nijar da Senegal da kuma Togo suka yi a birnin Yammai na Jamhuriyar Nijar.

Wannan taro ya bayyana kasashen dake fuskantar barazanar yunwar da suka hada da Burkina Faso da Mali da Nijar da kuma Senegal inda suka ce mutane kusan milyan uku da rabi ne ke bukatar abincin da zasu ci.