rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan ta Kudu

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kudirin cirewa Sudan ta kudu takunkumin sayen makamai

media
Wasu daga cikin mayakan yan tawayen Sudan ta kudu REUTERS/Goran Tomasevic

Amurka ta gabatar da wani kudiri a gaban kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya domin cirewa kasar Sudan ta kudu takunkumin sayen makamai, bayan kasar ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin shugaba Salva Kiir da shugaban yan tawaye Riek Machar.


Kudirin da wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya gani, ya bayyana damuwa kan cigaba da samun hare haren da bangarorin ke kaiwa bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiyar.

Kasar Amurka ce tafi taimakawa Sudan ta kudu tun bayan samun yancin kan ta daga Sudan a shekarar 2011.