rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu daga cikin yan wasan Faransa sun bayyana damuwarsu

media
Paul Pogba dan wasan tsakiyar Faransa Sky Sports

A dai-dai lokacin da faransawa da dama ke ci gaba da bayyana murnar su bayan nasarar kungiyar kwallon kafar kasar na tsallakawa zuwa mataki ko zagaye na karshe a gasar bayan doke kungiyar kwallon kafar Belgium da ci 1 da 0, akasarin manazarta da wasu daga cikin yan wasan sun bayyana cewa yanzu kam aiki na gaban su.


Dan wasan tsakiya Paul Pogba yan lokuta da kamala wasar, kalaman sa na farko shine yanzu aka soma gasar, domin indan aka yi tuni a lokacin gasar cin kofin Turai haka ta faru, Faransa ta tsallaka zuwa mataki na karshe,wanda yan wasan suka kasa lashe kofin.

Pogba ya bukaci karin hadin kan yan wasan kungiyar domin kaucewa sake fadawa cikin wani rudani mai kama da wacan lokaci.

Pogba ya bayyana cewa duk da nasarar da suka yi a karawar su da Belgium, kungiyar kwallon kafar Belgium ba karamar kungiya ba ce.