Isa ga babban shafi
Kamaru

Paul Biya zai sake neman shugabancin Kamaru karo na 7

Shugaban Kamaru Paul biya ya sanar da aniyar sa ta yin tazarce bisa kujerar shugabancin kasar.

Paul Biya, shugaban kasar Kamaru.
Paul Biya, shugaban kasar Kamaru. AFP
Talla

Karo na bakwai kenan da Paul Biya mai shekaru 85, zai tsaya takara a zaben shugabancin Kamaru wanda za a yi a ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa.

Cikin wani sako da ya aike ta shafinsa na twitter, shugaban na Kamaru, ya ce “ni ne zan zama dan takarar shugabancin kasar ku a zabe mai zuwa”

Cikin sakon nasa shugaba Paul Biya ya ce yana sane da tarin kalubalen da kasar ta Kamaru ke fuskanta, to amma yana neman hadin kan ‘yan kasar domin fuskantar matsalolin tare da magance su baki daya.

A halin yanzu Paul Biya ne shugaban kasa mai ci na biyu mafi dadewa a karagar mulki, bayan fara shugabantar Kamaru a shekarar 1982, wanda zuwa 2018 ya shafe shekaru 35 yana jagorantar kasar.

A halin yanzu shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema, shi ne shugaban kasa mai ci mafi dadewa bisa karagar mulki bayan shafe shekaru 38 yana jagoranci.

An haifi shugaba Paul Biya a ranar 13 ga watan Fabarairu na shekarar 1933, bayan kammala karatunsa na Firamare da Sakandare ne daga bisani ya tafi zuwa kasar Faransa, inda ya karanci fannin Shari’a, ya kumadawo gida a shekarar 1962.

A shekarar 1975 aka nada Paul Biya a matsayin Fira Ministan kasar Kamaru, daga bisani ne a shekarar 1982 ya karbi rikon shugabancin kasar daga hannun shugaba mai ci Amadou Ahidjo da ke fama da rashin lafiya.

A shekarar 1984 Paul Biya ya zama zababben shugaban kasar Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.