Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya 23 ne suka bata a Bama

Rahotanni daga Najeriya sun ce sojojin kasar 23 dake yaki da kungiyar boko haram ne suka bata lokacin da mayakan suka yiwa tawagar motocin su kwantar bauna a Bama.

Sojojin Najeriya bayan nasara a kan yan kungiyar Boko Haram
Sojojin Najeriya bayan nasara a kan yan kungiyar Boko Haram REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo daga bakin wani hafsan sojin dake Maiduguri cewar lamarin ya auku ne a kauyen Balagallaye a wajen garin Bama.

Jami’in sojin yace daga cikin sojojin da suka bata sun hada da manyan jami’ai 5 da kanana 18, yayin da suka rasa motoci 8.

Kamfanin dillancin labaran Faransar yace wani jami’in kungiyar yan kato da gora ya tabbatar da aukuwar lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.