rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Katsina

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Osinbajo na ziyarar jaje a jihar Katsina

media
Kimanin gidaje 200 suka rushe a ambaliyar jihar Katsina rfihausa

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Katsina don jajanta wa al'ummar jihar bisa ibtila'in ambaliyar ruwa da ya hallaka mutane kimanin 50, yayin da gidaje sama da 200 suka rushe, lamarin da ya raba dubban mutane da muhallansu.


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa kan aukuwar lamarin, in da gwamnatinsa ta yi alkawarin taimaka wa wadanda abin ya shafa.

Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina Aminu Waziri, ya ce an samu ibtila'in ne  a karamar hukumar Jibia sakamakon ruwan da aka tafka a ranar Lahadi a garuruwan Tundun Tikari da Dan Tudu da Unguwar Kwakwa da Unguwar Mai Kwari.

Rahotanni na cewa, ambaliyar ta kora gawarwakin mutane har cikin Jamhuriyar Nijar,  yayin da tuni aka yi jana'izar wadanda suka rasa rayukansu.

Jami’in ya ce ruwan ya kuma lalata gonakai da dama baya ga kashe daruruwan dabbobi.

Shugaban hukumar agajin gaggawan ya ce tuni aka tura jami’an agajin gaggawa domin taimakawa mutanen da yankin da abin ya faru.