Isa ga babban shafi
Habasha

Majalisar Habasha ta amince da dokar yi wa dubban 'yan kasar afuwa

Majalisar Habasha ta amince da shirin yi wa dubban ‘yan kasar Afuwa, wadanda a baya aka kama su da laifin tayar da rikici a sasan kasar.

Sabon Fira Ministan Habasha, Abiy Ahmed a zauren majalisar kasar da ke birnin Addis Ababa.
Sabon Fira Ministan Habasha, Abiy Ahmed a zauren majalisar kasar da ke birnin Addis Ababa. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Shirin afuwar ya shafi, mutane ko kungiyoyin da ake bincikarsu ko kuma aka yanke wa hukunci, bisa aikata laifukan cin amanar kasa, rashin mutunta kundin tsarin mulkin kasar, ko kuma daukar makamai domin adawa da gwamnatin.

Tun bayan kama aikin sabon Fira Ministan habasha Abiy Ahmed a watan Afrilu, ya bada umarnin sakin dubban fursunonin siyasar da aka tsare a baya, tare da bai wa batun tattaunawar sulhu da ‘yan adawa muhimmanci.

A farkon watan Yuli da muke ciki na shekarar 2018, Fira Minista Abiy Ahmed ya bada umarnin korar wasu shugabannin gidajen yarin kasar, sakamakon samunsu da laifin cin zarafin dan adam, kwanaki kalilan bayan da kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta wallafa wani rahoto da ke bayyana yadda ake cin zarafin fursunoni ta hanyar Fyade, da kuma azabtarwa, a wasu gidajen yarin kasar ta Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.