rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal Rwanda Afrika ta kudu China BRICS

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban China ya fara ziyara a Afrika

media
Shugaba Xi Jinping da kuma Macky Sall, a 2014 a birnin Pékin. ROLEX DELA PENA / POOL / AFP

A yau asabar shugaban China Xi Jinping ya isa birnin Dakar na kasar Senegal, matakin farko na ziyarar mako daya a wasu uku na nahiyar Afirka.


Wannan ne dai karo na uku da Xi Jinping ke gudanar da ziyara a Afirka a matsayinsa na shugaban kasa, inda bayan ganawa da shugaban Macky Sall a birnin Dakar, zai wuce zuwa birnin Kigali na Rwanda domin ganawa da shugaba Paul Kagame, sannan ya wuce zuwa Afirka ta Kudu domin halartar taron kasashen duniya masu samun habakar tattalin arziki wato Brics a birnin Johanneshurg.

China dai na cigaba da saka jari a kasashen nahiyar Afirka, inda alkaluma ke cewa akwai kamfanoni mallakin ‘yan kasar da yawansu ya haura dubu 10 a sassa daban daban na nahiyar.