Isa ga babban shafi
Chadi

Mayakan Boko Haram sun hallaka mutane 18 a Chadi

Rundunar sojin kasar Chadi ta ce mayakan Boko Haram sun hallaka mutane 18 a wani hari da suka kai kan wani kauye kudu da garin Daboua, da ke kan iyakar kasar da jamhuriyar Nijar.

Yankin tafkin Chadi, da ke fama da hare-haren mayakan Boko Haram.
Yankin tafkin Chadi, da ke fama da hare-haren mayakan Boko Haram. AFP Photo/PHILIPPE DESMAZES
Talla

Majiyar Sojin kasar wadda ta fitar da sanarwar a yau lahadi, ta ce mayakan na Boko Haram sun kai harin tun a ranar Alhamis da ta gabata, inda suka sace mata 10 tare da jikkata mutane 2.

A watan Mayu da ya gabata, akalla mutane 6 ne suka hallaka a wani hari da mayakan na Boko Haram suka kai kan wani shingen binciken ababen hawa na sojin kasar ta Chadi.

Harin dai ya rutsa ne da wasu jami’an gwamnatin Chadi 4 da kuma wani soja 1.

A ranar Asabar da ta gabata 21 ga watan Yuli na 2018, rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta sanar da samun nasarar hallaka wasu mayakan Boko haram 10, bayanda suka kai wa daya daga cikin sansanoninta hari a yankin kudu maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.