Isa ga babban shafi
DR Congo

An kawo karshen cutar Ebola a Jamhuriyar Congo

Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta sanar da kawo karshen barkewar cutar Ebola a hukumance, bayan makwanni 10 da sake bullar cutar wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 33.

Ebola ta kashe mutane 33 bayan sake bullarta a Jamhuriyar Demokradiyar  Congo
Ebola ta kashe mutane 33 bayan sake bullarta a Jamhuriyar Demokradiyar Congo AFP Photo/Junior D. Kannah
Talla

Ministan Kiwon Lafiyar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Oly Ilunga ya bayyana cewa, bayan shafe tsawon kwanaki 42 na sanya ido ba tare da samun ko mutum guda da ya kamu da cutar ba, yanzu haka suna bada sanarwar cewa, cutar Ebola ta kawo karshe a wannan kasa.

A baya bayan nan dai, cutar ta fara bayyana ne a yankin arewa maso yammacin Bikoro da ke kasar, in da nan take aka samun mutane 8 da suka riga mu gidan gaskiya a ranar 8 ga watan Mayu, yayin da a sau tara kenan da wannan cuta ke bulla a Congo tun daga shekarar 1976.

Labarin sake bullar cutar ya janyo hankulan kasashen duniya musamman ma lokacin da cutar ta isa birnin Mbandaka mai cike da hada-hadar jama’ar da yawanta ya haura miliyan 1.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun ce, irin wannan cuta mai yaduwa na da wuyan sha’ani a manyan birane idan aka kwatanta da kauyuka, abin da ya sa hankali ya tashi da jin labarin bullarta a Mbandaka.

Ebola ta yi sanadiyar mutuwar jumullar mutane sama da dubu 11 a kasashen yammacin Afrika da suka hada da Guinea da Liberia da Saliyo tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.