Najeriya na asarar Naira Biliyan 3 duk shekara saboda hadurra
Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya FRSC dakta Boboye Oyeyemi, ya ce kasar na tafka hasarar akalla Naira Biliyan 3 duk shekara sakamakon hadurran ababen hawa.
Wallafawa ranar:
Dakta Oyeyemi ya bayyana alakalumma ne, yayin taron jami’an kula da kiyaye hadurra na kasashen yammaci Afrika da ya gudana a kasar Senegal.
Shugaba hukumar kiyaye hadurran na Najeriya, ya ce kashi 38 daga ciki wadanda ke rasa rayukansu sakamakon hadurran ababen hawa a Afrika masu tafiya a kasa ne, yayinda a duniya kuma alkalumman ke kan kahi 19 ciki dari.
Kiddigar ta kara da cewa, kashi 23 na hadurran ababen hawa a duniya yana rutswa ne da mahaya Babura, kahi 22 masu tafiya a kasa, sai kuma 31 na yawan hadurran da ake samu a duniya da ke rutsawa da masu motoci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu