rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rahotanni Tarayyar Afrika ECOWAS CEDEAO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taron ECOWAS da ECCAS ya cimma kudurori 37 kan tsaro

media
Wasu daga cikin shugabannin kasashen Yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afrika, yayin taron hadin gwiwa kan shanin tsaro da kuma siyasa a Lome, babban birnin kasar Togo. Vanguard.ng

Shugabannin kasashen Yammacin Afrika ECOWAS da takwarorinsu na Tsakiyar Afrika ECCAS, sun kammala taron hadin-giwa da suka gudanar a birnin Lome na kasar Togo, tare da daukar muhimman kudurori har guda 37 domin tunkarar matsalar tsaro a yankunansu.

Daga cikin muhimman batutuwan da taron shugabannin ya tattauna akai, akwai rikicin manoma da makiyaya da kuma da kuma hana yaduwar makamai, kamar yadda ministan cikin gidan Najeriya Abdurrahman Dambazau ya bayyana cikin rahoton da wakilinmu Muhammad Kabir Yusuf ya aiko mana.


Taron ECOWAS ya kafa dokar magance rikicin Makiyaya da Manoma 30/07/2018 - Daga Kabir Yusuf Saurare

 

 

 

 

 

A yau Talata shugabannin kasashe mambobi a kungiyar gamayyar tattalin arzikin yankin yammaci Afrika ECOWAS ko kuma CEDEAO ke fara babban taronta karo na 53 a birnin Lome na kasar Togo.

Taron dai zai fi mayar da hankali kan rikice-rikice siyasa, da kuma matsalolin tsaro a kasashen Guinea-Bisau, Mali da kuma mai masaukin baki kasar ta Togo.