Isa ga babban shafi

Dukkanin 'yan takarar shugabancin Zimbabwe na ikirarin samun nasara

Yayinda aka soma tattara sakamakon Zaben shugabancin Zimbabwe, ‘yan takarar shugabancin kasar biyu, a yau Talata sun yi ikirarin cewa sun kama hanyar samun nasara da gagarumin rinjaye.

Dan takarar shugabancin Zimbabwe, kuma jaron jam'iyyar adawa ta MDC Nelson Chamisa, yayin kada kuri'a a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe. 30 ga watan Yuli, 2018.
Dan takarar shugabancin Zimbabwe, kuma jaron jam'iyyar adawa ta MDC Nelson Chamisa, yayin kada kuri'a a Harare, babban birnin kasar Zimbabwe. 30 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Zaben shugaban kasar shi ne na farko da ya gudana a Zimbabwe ba tare da tsohon shugaba Robert Mugabe ba, inda rahotanni suka ce an samu fitowar jama’a sosai.

Bayan soma kidayar kuri’un da aka kada ne shugaba mai ci da ke neman zarcewa Emmerson Mnangagwa, ya ce jam’iyyarsa ta ZANU-PF na samun rinjaye kan ‘yan adawa.

To sai dai a nasa martanin jagoran ‘yan adawa na jam’iyyar MDC Nelson Chamisa, ya ce ba shakkah suke da nasara a zaben da aka kada kuri’a cikinsa a ranar Litinin 30 ga watan Yuli na 2018.

Chamisa wanda ya sha bayyana zargin cewa gwamnatin Mnangagwa na shirin aikata magudi a zaben shugabancin kasar, ya ce zuwa yanzu sun kammala tattara akalumman kuri’un da aka kada daga mafi akasarin rumfunan zabe sama da dubu 10 da ake da su a kasar ta Zimbabwe.

Trust Matsilele, daya ne daga cikin wadanda suka sa ido kan yadda zaben ya gudana a ranar Litinin, wanda ya ce an yi zaben ba tare da samun tashin hankali ba, sabanin zabubukan da aka yi a baya.

Matsilele ya ce ana iya cewa an bai wa jama’a damar kada kuria’ a wannan karo ba tare da wata fargaba ba, sai dai watakila halaye na murdiya ko kuma rashin haske da za su iya bayyana daga bisani.

Kididdiga daga jami’an zaben kasar da na sa ido, sun ce an samu fitar akalla kashi 75% na yawan wadanda suka cancanci kada kuri’a a zabukan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.