rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.

Rahotanni Najeriya Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya ta bankado badakalar Naira biliyan 62 a kamfanin Inshorar Ma'aikata

media
Tuni Ministan kwadagon kasar, ya ce duk wanda aka samu da laifi zai dandana kudarsa. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Gwamnatin Najeriya ta bankado badakalar kudi da suka kai sama da Naira Biliyan 62 a hukumar inshoran ma’aikata na kasar da ake kira Nigeria Social Insurance Trust Fund, NSITF.A ranar 15 ga watan Fabararirun shekarar 2017 ne ministan kodago Chris Ngige ya nada komiti na musamman don gudanar da bincike kan harkokin da suka shafi kudin hukumar, bayan wani rahoto daga hukumar EFCC da ya bankado nuna wadaka da rashin bin ka’idoji wajen kashe kudin jama’a, da kuma zargin wasu manyan shugabannin NSITF da hannu dumu dumu a ciki.

Tuni Ministan kwadagon, ya ce duk wanda aka samu da laifi zai dandana kudarsa. Wakilinmu Muhammed Sani Abubakar ya gudanar da bincike kan lamarin, kuma ga rahotan da ya aiko mana.


Najeriya ta bankado badakalar Naira biliyan 62 a kamfanin Inshorar Ma'aikata 01/08/2018 - Daga Mohammed Sani Abubakar Saurare