Isa ga babban shafi

Zanga-zangar zargin magudin zabe ta barke a Zimbabwe

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya bukaci al’ummar kasar su kwantar da hankalin su a dai dai lokacin da ake ci gaba da zanga-zanga a wasu sassan kasar, sakamakon gaza bayyana sakamakon zaben da ya gudana a karshen mako.

Itama Jam’iyyar adawa ta MDC ta yi zargin hadin baki tsakanin jam’iyya mai mulki da hukumar zaben kasar don shirya magudin zabe.
Itama Jam’iyyar adawa ta MDC ta yi zargin hadin baki tsakanin jam’iyya mai mulki da hukumar zaben kasar don shirya magudin zabe. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Dubban masu zanga-zanga ne suka yi dandazo a ciki da wajen Harare babban birnin kasar bisa zargin aikata magudi a zaben wanda kawo yanzu aka gaza bayyana sakamakonsa.

Tuni dai jami’an tsaro suka fara amfani da hayaki mai sa hawaye dama harsasai don tarwatsa masu zanga-zangar wadda kawo yanzu aka tabbatar da mutuwar mutum guda wanda aka harba har lahira.

Masu zanga-zangar dai na kona hotunan jam’iyyar ZANU-PF mai shugabancin kasar inda cikin karaji suke cewa basa bukatar mayaudara.

Ko a jiya ma dai masu sanya idanu kan zabe na kungiyar Tarayyar Turai EU sun kalubalanci tsare-tsaren zaben na Zimbabwe, wanda ke matsayin na farko a kasar tun bayan dogon mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe da ya yi murabus a watan Nuwamba.

Itama dai jam’iyyar adawa ta MDC ta yi zargin hadin baki tsakanin jam’iyya mai mulki da hukumar zaben kasar don shirya magudin zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.