Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

An hana Moise Katumbi komawa gida Congo

Mahukunta a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun hana wa daya daga cikin masu adawa da shugaban kasar wato Moise Katumbi tsallaka iyakar kasar domin komawa gida.

Dan adawar Congo, Moïse Katumbi lokacin wata ziyara a birnin Kigali na Rwanda 27 ga watan afrilun 2018
Dan adawar Congo, Moïse Katumbi lokacin wata ziyara a birnin Kigali na Rwanda 27 ga watan afrilun 2018 Yasuyoshi CHIBA / AFP
Talla

Katumbi, wanda ya share tsawon kwanaki a Afrika ta Kudu, da farko ya nemi a ba shi izinin komawa kasar ta hanyar amfani da jirgin sama mallakinsa amma aka hana shi, daga nan ne kuma ya yi yunkurin tsallaka iyaka ta kasa domin isa a birnin Lubumbashi amma aka kange shi.

Katumbi mai shekaru 53 a duniya, yana fatan komawa gida domin tsayawa takarar neman shugabancin kasar a zabe mai zuwa, to sai dai kafin nan mahukunta sun yi barazanar cafke shi matukar ya sanya kafa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.