Mutane 23 sun mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a jihar Sakkwato
A jihar Sakkwato da ke tarayyar Najeriya, mutane 23 ne suka rasa rayukansu a daidai lokacin da suke kokarin tserawa daga wani hari da ‘yan bindiga suka kai wa kauyukansu.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mutanen sun hadu da ajalinsu ne lokacin da suke kokarin tsallaka wani kogi ta hanyar amfani da kwale-kwale domin komawa a kauyukansu da suka baro biyo bayan hare-haren da 'yan bindiga suka kai masu a kwanakin da suka gabata.
Lamarin ya faru ne a ranar alhamis, kuma mai magana da yawun rundunar 'yan sanda jihar Sakkwato DSP Codilian Wawei, ta shaida wa wakilinmu Faruk Yabo cewa, adadin mutane da ke cikin kwale-kwalen sun fi 50, kuma hatsarin ya faru ne a gundumar Gandi.
Tuni dai aka tabbatar da mutuwar mutane 23 a cewarta, an kwantar da wasu 8 a asibiti domin samun kulawa jami'an kiwon lafiya yayin da ake cigaba da neman wasu mutane 9.
Bayanai sun 17 daga cikinsu mata ne yayin da sauran 4 yara kanana ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu