Isa ga babban shafi
Masar

mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafar kasar Masar Essam El-Hadary ya yi ritaya

Shahararen mai tsaron gidan nan dan kasar Masar Essam El-Hadary,dan shekaru 45 a duniya, a marecen jiya litanin ne, ya bayyana kawo karshen aikinsa bayan da ya tsarewa kungiyar kwallon kafar Pharaons ta Masar gida har sau 159.

Essam El-Hadary a lokacin wasansu da Saudiya  25 yuni 2018
Essam El-Hadary a lokacin wasansu da Saudiya 25 yuni 2018 REUTERS/Darren Staples
Talla

Essam El-Hadary ya zama dan wasa mafi tsufa a tarihi, da ya buga wasan cin kofin duniya na bana farko a kasar Rasha.

Bayan da na jima ina nazari, tare da neman zabin Allah, na yanke shawarar janyewa daga wasanin duniya, kamar yadda dan wasa mafi tsufa na kungiyar ta kwallon kafar Pharaon ta kasar Masar ya sanar a shafinsaa na Facebook.

Anasa bangaren lokacin da yake tsokaci ta sahafinsa ba na Twitter fitacen abokin wasansa, dan wasan tsakiyar fagen kungiyar Liverpool Mohamed Salah, Cewa ya yi gwarzon da ya kafa tarihin tsawon shekaru masu armashi ya tafi ya barmu

A karkashin tutar kasar masar Essam El-Hadary ya lashe kofuna 4 a gasar cin kofin kwallon kafa ta nahiyar Afrika 1998, 2006, 2008 da kuma 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.