Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Ouattara ya yi wa fursunoni 800 afuwa

Shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya bayyana yi wa mutane kusan 800 da ke garkame a gidajen yarin kasar afuwa, cikinsu har da matar tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo, wato Simone Gbagbo.

Shugaban kasar Cote d'Ivoir Alassane Ouattara
Shugaban kasar Cote d'Ivoir Alassane Ouattara REUTERS/Luc Gnago
Talla

Shugaba Ouattara ya bayyana shirin afuwar ne a jawabin da ya yi wa al’ummar kasa a yammacin ranar Litinin dangane da bikin ranar samun yancin kan kasar da ke gudana a yau Talata.

Ouattara ya shaida wa al’ummar kasar cewar, nan gaba kadan za a saki Simone Gbagbo wadda a makon jiya kotun koli ta soke wanke ta da wata kotu ta yi kan zargin cin zarafin bil'adama.

Kotu ta daure matar tsohon shugaban kasar shekaru 20 a gidan yari a shekarar 2015 saboda samun ta da abin da ta kira katsalandan kan harkokin tsaron kasa da kai hari kan wata kasuwa da ke dauke da magoya bayan shugaba Ouattara a shekarar 2011 da kuma kitsa kai hari kan jami’an tsaro ta hannun kungiyar da ke dauke da makamai da ke goya wa mijinta baya.

Cikin wadanda za su amfana da afuwar har da matar tsohon ministan tsaro, Lida Kooassi da aka daure shekaru 15 da tsohon ministan gine gine, Assoa Adou da aka daure shekaru 4.

Shugaba Ouattara ya ce, ya sanya hannu kan dokar afuwar a ranar
Litinin, kuma nan bada dadewa ba, wadanda afuwar ta shafa za su koma gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.