Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Kabila ya zabi magajinsa a zaben Jamhuriyar Congo

Shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Joseph Kabila ya zabi tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Emmanuel Ramazani Shadary don maye gurbinsa a takarar zaben kasar mai zuwa, lamarin da ya kawo karshen rade-radin tazarcensa a kujerar mulki.

Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila ba zai yi tazarce ba a zaben shugabancin kasar mai zuwa ba
Shugaban Jamhuriyar Congo Joseph Kabila ba zai yi tazarce ba a zaben shugabancin kasar mai zuwa ba REUTERS/Kenny Katombe/File Photo
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da ya ya rage ‘yan sa’oi a rufe karbar takardun neman izinin shiga takara a zaben wanda zai gudana a ranar 23 ga watan Disamba na bana, zaben da masharhanta ke cewa, na da matukar muhimmanci ga makomar kasar mai yawan ala’umma miliyan 80.

Tun bayan da ta samu ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka na Belgium a shekarar 1960, Jamhuriyar Demokradiyar Congo ba ta taba samun walwalar mika mulki daga wata gwamnati zuwa wata ba cikin lumana.

Shugaba Kabila mai shekaru 47 ya shafe tsawon shekaru 17 yana jagorancin kasar, in da ya gaji mahaifinsa, Laurent-Desire Kabila da wani dogarinsa ya kashe bayan zargin sa da cin hanci da kuma keta hakkokin bil’adama.

Yanzu haka shugaba Kabila ba shi da damar yin tazarce bayan kammala wa’adi biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Mr. Shadary, shi ne Sakataren din-din-din na Jam’iyyar PPRD ta shugaba Kabila, yayin da gwamnatin kasar ta ce, za ta mara masa baya a yakin neman zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.