rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya

media
Mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da makamai REUTERS/Emmanuel Braun

Akalla sojojin Najeriya 17 mayakan Boko Haram suka hallaka a wani sabon hari da suka kai wani sansanin sojojin a yankin Arewa maso gabashin kasar.


Wata majiya ta jami'an tsaron ta sheidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa a ranar Alhamis mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da makamai, tareda kashe sojojin Najeriya, yayinda wasu suka bata a wannan harin da ya kasance na uku a kasa da wata guda.

A makon da ya gabata dai ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da damke wani kwamandan kungiyar Boko Haram da ta shafe lokaci mai tsawo tana neman sa ruwa a jallo.