Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Hukumar zaben Congo ta soma tattance 'yan takara

A Jamhuriyar Dimokkuradiyar Congo yan takara a zaben Shugabancin kasar 26 ne suka samu yi rijista tareda gabatar da takardun su zuwa hukumar zaben kasar. A daya geffen Shugaban kasar Joseph Kabila ya bayanna cewa ba zai tsaya takara ba, matakin da kasashen Duniya suka yaba da shi

Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Joseph Kabila,Shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo © AFP
Talla

Bayan da kasashen Duniya suka soma nuna farin cikin su bayan janyewar Shugaban kasar Joseph Kabila da sake neman takarar shugabancin Congo,

tun ranar 2 ga watan Agusta ne kotuna na musaman suka mayar da hankali domin fayyace daya bayan daya takardun yan takara 59.139 a zaben wakilan majalisa da zai gudana ranar 23 ga watan disemba, bayan haka dai ne hukumar zaben kasar za ta mayar da hankali ranar 11 ga wannan watan domin fitar da sunayen yan takara da suka dace su tsaya neman kujerar majalisa.

Bangaren takara na Shugabancin kasar yan takara 26 ne suka samu yin rijista , yan takara da suka hada da Antoine Gizenga, Adolphe Muzito, Amy Badibanga, Emmanuel Ramazani na kusa da Shugaban kasar kuma ministan tsaro, Felix Tshisekedi, Vital Kamere, Michel Okongo, Jean Pierre Bemba.

Daya daga cikin masu adawa da Shugaban kasar tsohon gwamnan Katanga Moise Katumbi da hukumomin suka haramtawa shiga kasar bai samu damar gabatar da takardun sa zuwa hukumar zabe ba, wanda magoya bayan sa ke ci gaba da yi tir da Allah wadai gani matakan tsaro da hukumomin suka dauka a kan iyakar kasar da Zambia don hana shi shiga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.