rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kamaru na binciken zargin kisan fararen hula

media
A cewar gwamnatin kasar za ta gudanar da bincike don ganin cewa bidiyon ba Farfaganda ba ce don yiwa gwamnatin shugaba Paul Biya bita da kulli. AFP

Gwamnatin kasar Kamaru ta ce tana gudanar da bincike kan wani sabon faifan bidiyon da ke nuna jami’an tsaron ta na harbe akalla fararen hula 12 a yankin arewa Mai nisa da ake fama da matsalar boko haram.


Kakakin gwamnati Issa Tchiroma Bakary ya ce gwamnati za ta gudanar da bincike duk da yake a baya an dade ana farfagandar bata mata suna kafin zaben shugaban kasar da za’ayi.

Kungiyar Amnesty International ta ce ta gudanar da bincike kan bidiyon da jin ba’asin shaidu da samun Karin bayanai ta tauraron dan adam da kuma nazarin makamai da kayan sojin da akayi amfani da su wadanda suka tabbatar mata cewar sojojin Kamaru ne.

Kungiyar ta ce an dauki hotan ne a kauyen Achigaya kafin watan Mayun bara.