rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yau ake kammala yakin neman zaben Mali

media
''Yan takara Ibrahim Boubacar Keïta da Soumaïla Cissé a zaben Shugabancin Mali zagaye a farko AFP

Yau juma'a ita ce ranar karshe ta yakin neman zaben shugabancin kasa zagaye na biyu a Mali, inda ake shirin fafatawa a wannan karo tsakanin shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Soumaila Cisse.


‘Yan takarar da suka zo a matsayin na uku da kuma hudu Aliou Diallo da Cheikh Modibo Diarra, kowanne ya bukaci magoya bayansa da kada kuri’arsa ga wanda ya ke so, ba tare da kulla kawance da sauran ‘yan takara kamar yadda aka saba gani a siyasar kasar ba.

A makon da ya gabata ne Ministan kula da yankunan kasar, Mohammed Ag Erlafk ya shaidawa al’ummar kasar cewar, sakamakon zaben da akayi zagayen farko ya nuna cewar, shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya samu kusan kashi 42 na kuri’un da aka kada, yayin da Soumaila Cisse ya samu kusan kashi 18.

Sakamakon farko  ya nuna cewar, dan kasuwa Aliou Diallo ya samu kusan kashi 8 na kuri’un da aka kada, yayin da tsohon ministan sufuri, Cheikh Modibo Diarra ya samu kashi sama da 7 da rabi.

Yan takara 24 suka fafata a zaben, yayin da masu kada kuri’u sama da kashi 43 suka shiga zaben a tashoshi 23,000.