Isa ga babban shafi
IOM-BAKI

IOM ta ceto baki 'yan kasashen Afrika ta yamma 128 daga hallaka

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da kaurar baki ta IOM ta sanar da ceto baki 'yan kasashen Afirka ta Yamma 128 da suka hada da mata da yara kanana a wani daji da ke kusa da iyakar Algeria.

Hukumar ta ce tuni aka ba da agajin gaggawa ga wadanda suka sha wahala saboda tafiyar kafa.
Hukumar ta ce tuni aka ba da agajin gaggawa ga wadanda suka sha wahala saboda tafiyar kafa. REUTERS/Jon Nazca
Talla

Hukumar ta ce daga cikin bakin akwai mata 8 da yara 14 da aka gano su a Assamaka, wani gari a Nijar da ke iyaka da Algeria.

Hukumar ta ce tuni aka ba da agajin gaggawa ga wadanda suka sha wahala saboda tafiyar kafa.

Binciken da hukumar ta gudanar ya ce bakin sun fito ne daga kasashe 11 da suka hada da Najeriya da Benin da Guinea da Cote d’Ivoire da Mali da Gambia da Liberia da Kamaru da kuma Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.