rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jami'an tsaro sun kashe mutane 40 a Habasha

media
Ana zargin jami'an tsaron Somalia da kai harin cikin Habasha kan 'yan kabilar Oromiya (Photo : Reuters)

Gwamnatin Habasha ta ce, akalla mutane 40 jami’an tsaro suka kashe a gabashin kasar da ke fama da rikicin kabilanci tsakanin mutanen yankin.


Kakakin jami’in da ke kula da yankin, Negeri Lencho ya ce, jami’an tsaro dauke da muggan makamai daga bangaren Somalia sun tsallake iyaka, in da suka kai hari gabashin Hararghe da ke yankin Oromiya.

Jami’in ya ce, bai san dalilin kai harin ba, amma kuma daukacin mutanen da aka kashe 'yan kabilar Oromiya ne.

A makon jiya, an samu wata mummunar zanga zangar ta kai ga matasa fasa shaguna da gidajen mutane don kwashe kayayyaki.