Isa ga babban shafi

Jami'an lafiya a Congo sun dauki matakan hana yaduwar Ebola

Hukumomin lafiya a birnin Goma na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sun yi gargadi kan gaisawar hannu da hannu ko kuma musayar hular kwano don kare al’umma daga kamuwa da cutar Ebola da ke gab da karasowa jihar.

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta samar da guraren wanke hannu a ilahirin sassan birnin na Goma don kasancewar kowa cikin tsafta.
Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta samar da guraren wanke hannu a ilahirin sassan birnin na Goma don kasancewar kowa cikin tsafta. REUTERS/Samuel Mambo
Talla

Annobar cutar ta Ebola wadda barkewarta a baya-bayan nan ta hallaka mutane 43 yanzu haka na ci gaba da yaduwa a sassan biranen da ke gabashin kasar yankin da ke ci gaba da fuskantar rikice-rikicen kabilanci dana jami’an tsaro.

Birnin Goma wanda ke da yawan jama’a akalla miliyan 1 na da tazarar kilomita 350 tsakaninsa da kan iyakar kasar da Rwanda kawo yanzu ba a samu barkewar cutar ba, amma hukumomi na ganin akwai bukatar a zauna cikin shiri la’akari da yadda ta isa garin Mangina da ake arewacin Kivu.

Haka zalika rahotanni sun ce yanzu haka akwai wadanda suka kamu da cutar a makwabcin birnin inda yanzu haka aka killacesu don kula da lafiyarsu tare da hana su cakuduwa da wasu don gudun yaduwar cutar.

Wani magidanci a birnin na Goma da ke sana’ar sayar da kayakin Masarufi ya ce dole ne su dauki dukkanin shawarwarin da jami’an kiwon lafiya za su basu don gudun kamuwa da cutar musamman a wannan lokaci da kowa ya ke a razane.

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta samar da guraren wanke hannu a ilahirin sassan birnin na Goma don kasancewar kowa cikin tsafta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.