Isa ga babban shafi
Mali

Cisse ya kalubalanci zaben Mali a kotun koli

Souma’ila Cisse, dan takarar jam’iyyar adawa a Mali da ya sha kaye a zaben shugabancin kasar da shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita ya lashe, ya shigar da kara kotun kolin kasar, inda ya bukaci ta soke zaben a dalilin tafka magudin da ya ce anyi.

Jagoran 'yan adawar Mali Soumaïla Cissé tare da magoya bayansa.
Jagoran 'yan adawar Mali Soumaïla Cissé tare da magoya bayansa. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

A ranar Alhamis da ta gabata, hukumar zaben kasar ta bayyana shugaba Keita ya lashe zaben da gagarumin rinjayen kashi 67 kan Cisse da ya samu kashi 33 a zagayen zaben shugabancin kasar na 2.

A cewar Souma’ila Cisse ba domin magudin da aka tafka ba, yana da yakinin zai lashe akalla kashi 51 na kuri’un da aka kada.

Sai dai tawagar sa ido kan zaben na Mali daga kungiyar tarayyar turai da wasu takwarorinta na ciki da wajen kasar, sun ce duk da cewa an fuskanci tangarda yayin gudanar da zaben da ya kai ga rufe rumfuna da dama, basu ga wata shaida da ke nuna an tafka magudin da ‘yan adawa ke zargi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.